1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Isra'ila sun mayar ta martanin hari

Zulaiha Abubakar
December 18, 2017

Sojojin Isra'ila sun kai hari a sansanin horas da 'yan kungiyar Hamas ta Falasdinawa wandanda suka wa Isra'ila hari da makami mai linzami.

https://p.dw.com/p/2pZY9
Gaza Proteste gegen Anerkennung USA Jerusalem
Hoto: Reuters/M. Salem

Rundunar Sojin Isra'ila ta kai wani hari sansanin horas da 'yan kungiyar Hamas ta Falasdinawa  a yau litinin,a wani abu da suka kira da mayar da martanin harin da 'yan kungiyar Hamas suka kai musu da makami mai linzami,sakamakon ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar ta Isra'ila da shugaban kasar Amirka Donald Trump ya yi a 6 ga wannan wata na Disamba.

Ya zuwa yanzu dai duka bangarorin basu fidda sanarwar irin ta'adin da aka yi musu ba,al'amarin dai ya faru gabanin ziyarar mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence a kudancin kasar ta Israila da kuma kasar Masar wacce ke iyaka da Gaza kuma ta ke fama da hatsaniyar siyasa.

A wani cigaban kuma wani mamba a zauren tsaron Firayim Minista Benjamin Natanyahu Zeev Elkin, ya bayyanawa manema labarai a wani gidan Rediyon kasar cewar sojin Isra'ila ba za su gajiya ba wajen mayar da martanin hari matukar Hamas bata daina kai mata hari da makami mai linzami ba.