Sojin Japan sun isa Sudan ta Kudu
November 21, 2016Kashin farko na sojojin kiyaye zaman lafiya 130 'yan kasar Japan sun sauka kasar Sudan ta Kudu a wannan Litinin don mara baya ga tawagar Majalisar Dinkin Duniya. An ba wa sojojin na Japan karin ikon amfani da karfi karon farko tun bayan yakin duniya na biyu. Sojojin na daga cikin tawagar sojoji 350 da Japan din za ta girke a Sudan ta Kudu karkashin inuwar Majalisar dinkin Duniya, wadda yawan dakarunta a kasar da yaki ya daidaita ya kai dubu 12. A cikin watan Disamba ake saran isar ragowar sojojin.
A makon da ya gabata gwamnatin Japan ta ba wa rundunar kasar izinin aiki waje tun bayan fara aiki da wasu dokokin tsaro a watan Maris duk da adawa mai karfi a cikin gida. Tun a shekarar 2012 Japan ke cikin tawagar Majalisar Dinkin Duniya amma ba su da izinin amfani da karfi.
Tun a watan Disamban 2013 Sudan ta Kudu ta fada cikin rikici lokacin da wata baraka tsakanin Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar ta rikide zuwa wani rikicin soji. Dubun dubatan mutane aka kashe sannan aka tilasta wa fiye da miliyan biyu barin gidajensu.