1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Najeriya na zargin UNICEF

Abdul-raheem Hassan
December 14, 2018

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da soke ayyukan asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a yankin Arewa maso Gabashin kasar bisa zargin tallafawa 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/3A99V
Kamerun Symbolbild Soldaten im Norden ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta zargi wasu jami'an UNICEF da horas da masu taimakawa 'yan ta'adda da bayanan sirri.

Kawo yanzu dai babu martani daga bangaren UNICEF kan matakin da sojojin Najeriyar suka dauka. A baya dai asusun ya koka kan yadda ayyukan Boko Haram ke tasirin hana dubban yara kanana karatu a arewacin Najeriya musamman yankin Arewa maso Gabashi.

Jihohin da ke Arewa maso Gabashin kasar na fuskanctar munanan hare-haren Boko Haram sama da shekaru tara, abinda kungiyoyin agaji na kasa da kasa ke dangatawa da munanan mawuyacin hali a duniya.