Sojin Pakistan sun kashe ´yan Taliban a Waziristan
July 22, 2007Talla
Rundunar sojin Pakistan ta kashe sojojin sa kai na Taliban 13 a arewacin yankin Waziristan dake kan iyaka da Afghanistan. Wata sanar da sojin gwamnati suka bayar yau lahadi ta yi nuni da cewa jiya da daddare wasu gungu-gungu na sojojin sa kai dauke da makamai sun yi kokarin afkama sansanonin soji da dama to amma an bankado wannan makarkashiya. Kakakin soji Manjo janar Waheed Arshad ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa dakarun sa sun kasance cikin shirin ko-takwana, inda suka mayar da martani kuma suka kashe ´yan tawaye 13.