An sami sojoji da laifin kashe abokan aikinsu
November 18, 2018Talla
Akwai wasu da suka sami rauni a artabun da ya biyo bayan sabanin da aka samu a tsakanin bangarorin biyu.Tun bayan da rikicin kasar ya kazance, aka kuma tsugunar da rundunar wanzar da zaman lafiya, ake yawan samun barkewar fada inda sojojin ke kashe juna.
Majalisar Dinkin Duniya na da akalla jami'an wanzar da zaman lafiya dubu goma sha biyu da ta tura Afirka ta Tsakiya.
A makon da ya gabata majalisar ta amince da ci gaba da barin sojojin duk da sukan da ake musu na nuna gazawa a aikin tabbatar da tsaro.
An kwashi sama da shekaru shida ana fama da tashe-tashen hankula da ya tilastawa mutum sama da miliyan hudu rasa matsuguni.