Sudan: Yarjejeniyar raba madafun iko
August 17, 2019Talla
Hukumomin mulkin soja na rikon kwarya a Sudan sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar na'am game da batun rarraba mukamai tsakanin jami'an sojan kasar da masu bore na kungiyoyin fararen hula a wannan Asabar, lamarin da ya kawo karshen zaman doya da manjan da bangarorin soja da masu bore suka shafe fiye da watanni suna yi a kasar.
Tuni dai yarjejeniyar ta kai ga tabbatar da raba mukamai na majalisar zartarwar kasar ta rikon kwarya wacce daga yanzu za ta kumshi sojan da na farar hula.
Akalla kawo yanzu fararen hula uku ne dukanninsu jagororin masu boren kasar ta Sudan suka samu damar shiga cikin gwamnatin inda za su tafiyar da ayyukansu kafada da kafada da sojojin da ke jagorancin gwamnatin ta rikon kwarya.