Sojoji na tarwatsa masu bore da karfi a Sudan
June 3, 2019Talla
Hukumomin mulkin soji a kasar Sudan sun tarwatsa zaman dirshan da masu fafutukar tabbatar da dimukaradiyya ke yi a gaban hedikwatar majalisar gudanarwar kasar.
Kungiyar kwararrun ma'aikata ta Sudan ta yi tir da matakin da sojojin ke dauka kan kungiyoyin masu zanga-zanga, tare da karfafa wa al'umma gwiwa na ci gaba da yi wa sojojin matsin lamba har sai sun mika mulki ga farar hula.
Tun a watan Disemban 2018 ne 'yan Sudan suka fara tada kayar baya kan tsadar rayuwa da kasar ke ciki, lamarin da ya kawo karshen mulkin tsohon Shugaban kasar Omar Hassan el-Bashir na tsawon shekaru 30 a watan Afirlun 2019.