1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kwace masallaci daga IS a Libiya

Abdul-raheem HassanAugust 22, 2016

Sojojin da ke marawa gwamnatin Libiya baya da na Amirka sun kwace iko da masallaci da gidan yari daga mayakan IS a birnin Sirte na kasar Libiya.

https://p.dw.com/p/1Jmf5
Libya - The Battle for Sirte - Make no prisoners
Hoto: DW/K. Zurutuza

Dakarun da ke yin biyayya ga gwamnatin kasar Libiya, sun sanar da yin nasarar kwace iko da wani katafaren masallaci da wani gidan yari da ke birnin Sirte daga hannun mayakan IS.

Wannan dai na zuwa ne a wani sabon sumame da dakarun suka kaddamar a karshen mako a babban sansanin 'yan bindigan da nufin kakkabe su daga tsohon tungarsu da ke birnin Sirte.

Dakarun da ke fafatawa tare da taimakon sojojin Amika da ke jibge a arewacin kasar Libiya, na ayyana samun nasarar karya lagon mayakan tun bayan da suka kaddamar da sumame a birnin na Sirte watanni uku da suka gabata.

To sai dai ana hasashen sauran mayakan da ke sajewa a wasu wurare za su ci gaba da kai farmaki a wuraren gwamnati da ma sansanonin jami'an tsaro da nufin daukar fansa.