Sojojin Amirka sun kai sabon hari kan IS a Iraki
March 26, 2015Talla
Sojojin kawancen yaki da mayakan kungiyar IS masu da'awar kafa daular Islama, sun sake kai farmaki kan sansanonin masu ikirarin jihadin a Iraki. Kakakin ma'aikatar tsaro a birnin Bagadaza ya ce jiragen saman yakin karkashin jagorancin Amirka sun kuma samu tallafi daga sojojin Iraki. A ranar Laraba ma Amirka ta kai hare-hare a birnin Tikrit da ke zama mahaifar tsohon shugaban Iraki Saddam Hussein. Tun a cikin watan Yunin bara mayakan IS suka mamaye birnin na Tikrit, kuma tun kimanin makonni hudu ke nan sojojin Iraki ke kokarin karbe iko da birnin.