Sojoji na daga cikin 'yan gudun hijirar Habasha
November 11, 2020Sojojin gwamnati na daga cikin dubban 'yan gudun hijira da suka tserewa rikicin kasar Habasha zuwa Sudan mai makwabtaka da kasar. Wani jami'in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, Sudan ta karbi akalla 'yan gudun hijira kimanin dubu goma da suka hada da mata da yara da kuma sojojin gwamnati dari biyar da suka yi sarenda tare da mika wa gwamnati makaman hannunsu.
Sudan ta baiyana damuwa kan halin da za a tsinci kai idan fadan ya ci gaba, wannan yasa take tunanin rufe kan iyakar kasar don hana kwararar 'yan gudun hijirar da ke tserewa barin wutan da ake yi.
Tuni Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta soma aikin agazawa dubban da rikici a tsakanin bangaren gwamnatin Firaiminista Abiy Ahmed dana adawa na 'yan Tawayen Tigray na TPLF suka haifar, tashin hankalin da ake ganin idan ba a gaggauta daukar matakin maganceta ba, ka iya rikidewa zuwa yakin basasa.