1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Isra'ila dana Hamas Huɗu sun rasu a yankin Gaza

March 27, 2010

Bayan bata kashi, rahotannin dake fitowa daga yankin na cewar anga Tankunan Sojojin Isra'ila na nausawa zuwa kusa da kan iyakan Gaza da Isra'ila tare da harbi zuwa garin Khan Yunis na kan iyaka

https://p.dw.com/p/MfdR
Wani Tankin yaƙin Sojojin Isra'ila a kan iyakan zirin GazaHoto: AP

Mutane Huɗu sun rasu sakamakon wani fito na fito tsakanin Jami'an tsaron Isra'ila da kuma na dakarun Sojin Hamas a yankin zirin Gaza a jiya juma'a. Biyu daga cikin wa`yanda suka rasun Dakarun Sojin Israila ne, a yayin da sauran ke zama na Hamas da akace suna dasa Bama-bamai kusa da kan iyakan yankunan ɓangarorin biyu. Bayan bata kashi, rahotannin dake fitowa daga yankin na cewar anga Tankunan Sojojin Isra'ila na nausawa zuwa kusa da kan iyakan Gaza da Isra'ila tare da harbi zuwa garin Khan Yunis na kan iyaka. A jiya ne dai Firaminista Israila Benjamin Netanyahu ya gana da majalisar ministocin sa da nufin tattauna kace nacen dake wakana tsakanin Isra'ila da Amurka, sakamkon matakin Isra'ilan na cigaba da gina sabbin matsugunai a yankin gabashin birnin ƙudus. A waje ɗaya kuma, a yau Asabar ake fara taron ƙungiyar ƙasashen Larabawa a ƙasar Libya. Wannan dai shine karon farko da ake gudanar da taron a Libya, wanda shugabanta Muammar Ghaddafi yasha sukan ƙasashen na Larabawa bisa gazawar su na ɗaukan matakan kawo ƙarshen matsalar Palasɗinawa. A lokacin wannan taro shugabannin zasu fito da matsayin su game da ƙoƙarin da Isra'ila keyi naci gaba da gine-gine a yankin birnin Ƙudus, duk kuwa da gargaɗi da kuma adawa daga  ƙasashen duniya ciki harda Amurka. Taron zai samu halartar Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon da Firaministan  Italiya Silvio Berlusconi dana Turkiya Recep Tayyip Erdogan.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammad Abubakar