1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta bukaci al'ummar Gaza da su koma kudanci.

Binta Aliyu Zurmi
October 29, 2023

Dakarun sojin Isra'ila sun umurci al'ummar Gaza da su koma yankin kudancin Zirin inda za a fadada isar musu da kayayakin agajin.

https://p.dw.com/p/4YA5C
Israel Tel Aviv | Armeesprecher Daniel Hagari
Hoto: Gil Cohen-Magen/AFP/Getty Images

A sanarwar da mai magana da yawuun sojojin na IDF Daniel Hagari, ya ce daukacin al'ummar da ke yankin da ake barin wuta su gaggauta barin wurin zuwa inda aka kebe musu domin samun abinci da magunguna da ruwan sha.

 

Ya kara da cewar yankin tsakiyyar Zirin ya zama fagen daga, kuma agajin da kasashen Masar da Amurka ba za su isa can ba.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Firaministan Isra'ila Benjamin Nathenyahu ya bayyana cewar wannan yakin da kungiyar Hamas zai dauki lokaci ana yin shi, wanda kuma ya sha alwashin sai ya ga bayansu.

Kungiyar Hamas ta fidda sanarwar cewar an hallaka dinbin fararen hula a sabon harin daren jiya a wasu sansanin da suke neman mafaka.

Ya zuwa yanzu sama da fararen hula dubu 8,000 ne aka tabbatar da mutuwarsu tun bayan barkewar rikicin makwanni 3 da suka gabata.