Sojojin kawance a Afghanistan sun kashe mayakan Taliban akalla 80
June 24, 2006Talla
Rahotanni daga Afghanistan sun ce dakarun kawance dake karkashin jagorancin Amirka sun samu nasara a farmakin da suke kaddamar kan ´yan tawayen kungiyar Taliban. Kakakin rundunar Amirka ya ce an kashe ´yan tawaye fiye da 80 musamman a kudancin kasar ta Afghanistan. A batakashin da aka kwashe sa´o´i da dama ana yi a jiya a kusa da garin Mirabad dake lardin Uruzgan an halaka akalla ´yan tawaye 40.