Sojojin Libya sun fatattaki IS daga tsakiyar birnin Sirte
August 11, 2016Kakakin sojojin Libya da ke fafatawa a birnin Sirte Kanal Mohammed al-Ghasri ya ce kungiyar IS ba ta da karfin dakarun da za su iya turje wa dakarun Libya a Sirte bayan da sojojin Libya suka sake kwace iko da cibiyar babban taro da ke tsakiyar birnin, inda 'yan tarzoma suka taba kafa bakar tutarsu ta Jihadi. Kanal Mohammed al-Ghasri ya ce yanzu an gama da mayakan na IS a wannan birni.
Ya ce: "A iya saninmu dai an yi gumurzu na karshe bayan mun karbi iko da cibiyar taro ta Ouagadougou kuma a garemu IS ta kare. Za su iya kokarin tserewa ko kashe kansu, amma ba su da karfin da za su iya fuskantar dakarunmu. Ga ra'ayin soja, IS ta kau bayan mun karbi iko da cibiyar ta Ouagadougou."
A wannan Alhamis dai dakarun Libya sun mamaye yankunan da suka kwace daga IS suna kuma tono nakiyoyin karkashin kasa a kewayen cibiyar taron da ke a birnin na Sirte.