Sojojin Majalisar Dinkin Duniya a Afirka
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da rage yawan sojojin majalisar a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, da kuma kara wa'adin aikin sojojin zuwa shekara guda.
Kwango: Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya mafi girma a Afirka
Tun a 1999 dakarun Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin tabbatar da tsaro a Arewa maso Gabashin Kwango. MONUSCO na yaki da ‘yan tawaye domin kare fararen hula. Tare da sojoji sama da dubu 22, da kuma kasafin kudi na shekara kimanin biliyan daya da rabi, ita ce runduna mafi girma kana kuma mafi tsada ta Majalisar Dinkin Duniya, sai dai duk da nasarori, har yanzu ana samun tashin hankali a kasar.
Dafur: Gaza magance tashin hankali
UNAMID runduna ce ta hadin gwiwa tsakanin kungiyar AU da Majalisar Dinkin Duniya. Aikinta shi ne wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur na Sudan. Masu saka ido a kan al’amura na ganin cewa rundunar ba ta yi nasara ba. Wani kwararre a kan harkar tsaro Thierry Vircoulon ya ce abin da ya kamata shi ne kwamitin ya bi hanyoyi na siyasa a maimakon kashe biliyoyin daloli wajen tura sojoji.
Sudan ta Kudu dauke kai domin gudun yaki
A lokacin da aka fara yakin Sudan ta Kudu, mutane kimanin dubu 63 da ke zaune a cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun fice. A gunsu dakarun UNMISS sun fi ba da kariya, kana yayin fadan da aka fafata a cikin watan Yuli na shekara ta 2016 tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawaye, dakarun majalisar ba sa shiga tsakani kuma ba sa amsa kiran ceto, gara babban kwamandan rundunar dan Kenya ya tafi.
Mali: Rundunar Majalisar Dinkin Duniya mafi fuskantar hadari
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya na aikin lura da mutunta yarjejeniyar zaman lafiyan da aka cimma tsakanin gwamnati da ’yan tawaye, koda yake wasu kungiyoyin ta’adda ba su sanya hannu ba. Suna kai hare-hare. Ana yi wa MINUSMA kallon rundunar majalisar mafi fuskantar hadari a duniya. Jamus na da sojoji 787 da kuma jiragen yaki a kasar, ta yi wu agaji mafi girma da Jamus ta bayar a waje ke nan.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tabargazar fyade na daukar hankali
MINUSCA a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba ta taimaka ba wajen kare mutuncin Majalisar Dinkin Duniya a Afirka. Tun a 2014 akwai sojoji dubu 10 da ’yan sanda 1800.Tun farko Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi fama da yakin basasa, kana akwai zarge-zarge da ake yi wa sojojin Majalisar Dinkin Duniya na cin zarafin yara kanana da mata ta hanyar yi musu fyade.
Tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin yammaci na Sahara
Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin yammacin Sahara na aiki tun da dadewa. Tun a 1991 MINURSO ta yi kokarin cimma tsagaita wuta tsakanin Maroko da ‘yan tawayen Polisario, da ke neman 'yancin kai, yankin da Maroko ta mamaye a 1976. A 2016 Maroko ta kori jami’ian MINURSO farar hula 84, bayan da babban sakataran majalisar ya ce Marokon ta yi mamaya a yanki.
Cote d'Ivoire karshen wa'adin rundunar wanzar da zaman lafiya cikin lumana
Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Cote d'Ivoire ta cika wa’adinta bayan shekaru 14, a ranar 30 ga watan Yuni na shekara ta 2017 wa’adin rundunar ke cika. Tun daga shekara ta 2016 aka fara janye sojojin rundunar. Tsohon sakataren majalisar Ban Ki Moon ya ce babban ci gaba ne ga majalisar da ma Cote d’Ivoire. Bayan janyewar sojojin, za a san ko rundunar ta cimma nasara.
Liberiya: Kokarin janye rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya
Rundunar rundunar wanzar da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Laberiya kamar a Cote d’Ivoire nan gaba kadan sai labari. Za a kawo karshenta a cikin shekara ta 2017. Tun lokacin da aka kawo karshen yaklin basasar kasar na shekaru 14, rundunar UNMIL ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Laberiya. Bayan annobar da kasar ta yi fama da ita ta Ebola da ta haddasa asarar rayuka, aikinta ya kammala.
Sudan da Ethiopia dukkaninsu na yunkurin samar da zaman lafiya
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya na UNISFA na yin sintiri a Abyei. Sudan da Sudan ta Kudu na yin jayayya a kan wani yanki da ke tsakaninsu. Akwai sojoji 4000 na majalisar galibi ‘yan kasar Ethiopia cikin rundunar. Ethiopia kan tura sojojinta wajen aikin tabbatar da tsaro a cikin kasashen duniya. Sai dai kungiyoyin kare hakin dan Adam na zargin sojojin Ethiopia da laifin take hakin dan Adam din.
Somalia: Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Tarayyar Afirka AU, wani abin misali?
Aikin samar da zaman lafiya a Somaliya na karkashin kulawar AU tare da tallafin Majalisar Dinkin Duniya AMISON a kokarin rage barazanar ayyukan ta’addanci daga kungiyar Al-Shabaab a yankin na kahon Afirka. Aikin rundunar shi ne samar da kwanciyar hanakali da ya dace, domin ci gaban zaman lafiya. Kasashen Ethiopia da Burundi da Djibuti da Kenya da Yuganda dukkaninsu na da sojoji a cikin rundunar.