Sojojin Mali sun ce sun gano kabari na bai daya a Kidal
November 19, 2023Talla
Rundunar sojin Mali ta ce ta gano wani kabari na bai daya a Kidal da ke yankin Arewa maso gabashin kasar, mako guda bayan kwato garin daga hannun Abzinawa 'yan tawaye. A cikin wata sanarwar da ta fitar a Bamako, rundunar ta ce kabarin na nuna irin ta'asar da wadanda ta danganta da marasa imani suka aikata, amma ba tare da bayar da karin bayani ba.Karin bayani:
Hukumomin na Mali sun bayyana cewar suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda ke hannu a kashe-kashen domin hukunta su. Tun a ranar 14 ga watan Nuwamba ne, Mali ta yi nasarar mayar da Kidal karkashin ikonta shekaru tara bayan da ta kasance tungar 'yan awaren Abzinawa wadanda suke bijerwa wa hukumomin Bamako.