1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Najeriya sun halaka fararen hula bisa kuskure

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 25, 2024

Mutanen jihar Sokoto sun shiga zullumi da fargaba, kasancewar karamar hukumar Silame na cikin kananan hukumomi 4 da 'yan ta'addan Lakurawa suke gudanar da harkokinsu.

https://p.dw.com/p/4oZkB
Sojojin Najeriya
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Ana fargabar mutuwar mutane 6 a Najeriya, bayan da jirgin saman sojin kasar da ke yakar 'yan ta'addan Lakurawa ya yi ruwan bama-bamai a kan fararen hula bisa kuskure, a kauyen Gidan Sama da Tunga Runtuwa da ke karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

Wakilinmu Ma'awiyya Abubakar Sadiq ya rawaito mana cewa wasu mutanen garin sun shaida masa cewa ba a kai ga yi wa mamatan sutura ba, inda ake jiran gwamnan jihar Sokoto.

Mutanen kauyen sun shiga zullumi da fargaba, kasancewa karamar hukumar Silame na cikin kananan hukumomi 4 da 'yan ta'addan Lakurawa suke gudanar da harkokinsu.

Karin bayani:Rundunar sojin Najeriya ta kammala hada rahoton kisan al'ummar Tudun Biri

A wani labarin kuma rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da jikkatar wasu mabiya addinin kirista da dama bayan da wata motar safa makare da hatsi ta kutsa cikinsu, a daidai lokacin da suke tattakin bikin Kirsimeti a jihar Gombe.

Karin bayani:Fashewar tankar mai ta haddasa mace-mace a Jigawa

ASP Buhari Abdullahi shi ne mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Gombe, ya shaidawa wakilinmu Al'amin Sulaiman Muhammad cewa ya zuwa yanzu dai babu rahoton asarar rai sakamakon hadarin.