Sojojin Nijar da na Amirka sun mutu a cikin Nijar
October 5, 2017Wata majiya ta tsaro ta kasar ta Nijar ta shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP cewa, sun yi rashin sojoji da dama a yankin jihar Tillabery mai makwabtaka da kasar Mali ba tare da bada wani adadi ba. Sai dai rundunar sojojin Amirka a Afirka ta Africom ta tabbatar da mutuwar sojojin Amirka guda uku, wasu kuma sun jikkata, yayin da ita ma jaridar New York Times ta kasar Amirka ta tabbatar da mutuwar sojojin na Amirka uku yayin da kuma wasu guda biyu da suka samu raunuka.
Mai magana da yawun fadar shugaban Amirka Sarah Sanders ta sanar wa manema labarai a birnin Washington cewa Shugaba Donald Trump ya sami labarin harin na Nijar ba tare da ta yi wani karin bayani ba.
A tsakiyar watan Satumba ne gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin jihar Tillabery da ke yammacin kasar da kuma Diffa da ke gabashi. Sai dai ya zuwa yanzu babu wani bayani daga hukumomin na Jamhuriyar Nijar.