Sojojin Nijar sun mayar da martanin wani harin Boko Haram
February 9, 2015Wata majiyar sojin Nija ta ce mayakan kungiyar Boko Haram ta Najeriya sun kai hari kan wani gidan kurkuku a kan iyakar Nijar amma an fatattake su. Harin shi ne na uku a jere cikin kwanaki hudu da Boko Haram ta kai a garin Diffa, kuma ya zo ne a lokacin da 'yan majalisar dokokin Nijar ke shirin kada kuri'a ko kasar ta shiga cikin kawancen yaki da masu ta da kayar bayan daga Najeriya. Majiyar ta ce bayan an fatattaki 'yan Boko Haram yanzu haka ana aikin tsabtace wurin. Majiyar ta fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa an girke sojojin Nijar kusan 3000 a wannan yanki na kan iyaka. A ranar Asabar gwamnatocin kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya da kuma Benin sun amince su kafa wata runduna mai dakaru 8700 da za su yaki Boko Haram.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe