Sojojin Senegal ne aka kashe a Darfur
April 2, 2007Talla
Rahotanni daga yankin darfur sunce dukkan dakarun AU 5 da aka kashe a Darfur yan kasar Senegal ne.
Kakakin rundunar sojin Senegal a Darfur din Antoine Wardini yace sojojin biyar suna daga cikin dakarun senegal 538 dake karkashin AU a Darfur wadanda suke gadin wani wajen ban ruwa a bakin iyaka yankin da Chadi.
Wardini yace kashe wadannan sojoji ba zai dakushe kokarin kasar ta Senegal ba na tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Kakakin AU Nourudden Mezni yace an kashe yan bindiga uku cikin musayar wutar haka kuma dakarun na AU suna nan suna binciken gawarwakin wadannan yan bindiga gano inda suka fito.