Hanyoyin neman kawo karshen rikicin siyasar Sudan
April 30, 2019Talla
Sojojin da ke rike da madafun iko a Sudan sun tabbatar da cewa suna shirye da ci gaba da tattaunawa da 'yan adawa domin tantance makomar kasar. Mataimakin shugaban gwamnatin mulkin ta wucen gadi Manjo-Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya bayyana haka inda ya ce suna neman hanyar ganin kawo karshen zaman dirshen da masu zanga-zanga ke yi cikin tsanaki da kwanciyar hankali.
Masu zanga-zanga na neman ganin kafa gwamnati ta fararen hula domin tsara mika mulki tun bayan nasarar da masu zanga-zangar suka samu ta kawar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir ranar 11 ga wannan wata na Afrilu, bayan da ya shafe kimanin shekaru 30 yana mulkin kama karya a kasar ta Sudan.