Sudan: Bude wuta kan masu bore
June 3, 2019Kimanin mutane uku ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a yunkurin sojoji na tarwatsa masu zanga-zangar a Sudan. 'Yan adawar kasar sun zargin sojojin da rashin mutunta yarjejeniyar da suka cimma da masu zanga-zangar tun bayan kifar da gawamnatin tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir. Wannan sabuwar takaddama dai, ta sake jefa shakku kan komawar kasar bisa tafarkin dimukuradiyya. A Khartoum jami'an tsaron sun toshe manyan hanyoyi don hana masu zanga-.zangar fitowa, matakin da ya haifar da tsaiko a babban birnin kasar da ke shirye-shiryen shagulgulan sallah karama.
Fathi Mohammed Abdoo, daya daga cikin jagoran masu zanga-zanga ya ce "Muna gayyatar dukkannin 'yan Sudan da su halarci sallar idin don su yi amfani da damar su nuna wa duniya halin da kasarsu take ciki."
Tuni jagororin masu zanga-zangar suka dora alhakin kisan 'yan uwansu kan sojojin da ke biyayya ga gwamnatin mulkin sojan, duk da yake a hannu guda sojojin sun ce tura ce ta kai su bango, inda suka ce daga cikin masu zanga-zangar wasu na saba ka'ida ta hanyar lalata motocin mutane da satar dukiyoyin jama'a. A watan Disamba na shekarar 2018 da ta gabata ne dai, al'ummar ta Sudan suka fara tada kayar baya kan tsadar rayuwa, zanga-zangar da ta kawo karshen mulkin tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir na tsawon shekaru 30.