Sojojin Turkiya sun kai hari kan 'yan awaren Kurdawa
September 7, 2015Talla
Sojojin Turkiya sun kaddamar da farmaki da sanyin safiyar wannan Litinin kan sansanoni 13 na 'yan awaren Kurdawa, kwana guda bayan harin bam da ya hallaka sojoji 15 yayin da wasu da dama suka samu raunika.
Jim kadan bayan harin na 'yan aware Firaminista Ahmet Davutoglu ya katse kallon kwallo domin gudanar da taron gaggawa, inda daga bisani aka tura jiragen saman yaki biyu da suka mayar da martani. 'Yan awaren na Kurdawa sun dade suna takun saka da gwamnatin kasar ta Turkiya.