1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya ƙasar Taliban?

April 17, 2010

An kwatanta Somaliya da wata ƙasa ta ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini kamar irin su Taliban

https://p.dw.com/p/MyrA
Sojan sa kai na ƙungiyar Al-Shabaab a birnin MogadishuHoto: AP

Za mu fara ne da sharhin da jaridar Berliner Zeitung ta rubuta game da Somaliya tana mai kwatanta ta da wata ƙasa ta Taliban. Ta ce saboda 'yan Islama dake iko a kusan ko-ina cikin birnin Mogadishu sun ayyana waƙoƙi a matsayin babban zunubi, yanzu dukkan tashoshin rediyo sun biyewa umarnin masu tsattsauran ra'ayin inda suka daina buga waƙoƙi domin fargabar cin zarafi da kisa. Ta ce wannan haramcin yayi tuni da lokacin mulkin Taliban a Afganistan. Jaridar ta ƙara da cewa wannan alama ce yadda kafofin yaɗa labaru a Somaliya ke rugujewar saboda rashin ƙwararan tsare-tsare na ƙasa. Ta ce ana tursasawa 'yan jarida na ciki da na waje kana kuma babu alamun kai musu ɗauki. Tarayyar Turai ta yi niyar horas da sojojin gwamnati 2000 a cikin watanni 12 masu zuwa, to amma sojojin tarayyar Afirka 4000 sun kasa ma tsaron tashar jirgin ruwan Mogadishu, ta yaya sojoji 2000 za su iya yin wani kataɓus?

A bara kaɗai an yiwa 'yan jarida tara kisan gilla a Somaliya sannan 39 sun tsere saboda barazana ga rayuwansu. Jaridar Süddeutsche Zeitung kenan tana sharhi ga mawuyacin halin da 'yan jarida suka samu kansu ciki a Somaliya. Ta ce ba kawai waƙoƙi aka haramta rediyoyin bugawa, a'a 'yan Islama na matsawa tashoshin da su watsa shirye-shiryen farfagandar aƙidojin ƙungiyoyin na masu tsattsauran ra'ayi.

Fußball WM Südafrika 2010 Pretoria Werbung
Allon tallar gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya a Afirka Ta KuduHoto: DW

A dole za a barsu a waje, taken jaridar Tageszeitung kenan tana tsokaci ga gasar cin kofin ƙwallon ƙafar duniya da za a yi a Afirka Ta Kudu. Ta ce ga ɗaukacin 'yan ƙasar murna za ta koma ciki domin fatansu na samun wata garaɓasa sakamakon gasar kofin duniya, zai tsaya mafalki ne. Ta ce saboda biyewa dokokin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, daga 11 ga watan Yuni Afirka Ta Kudu ta haramta buɗe wasu filayen wasa ga talakawan ƙasarta sannan masu ƙananan sana'o'i a kusa da filayen wasan ƙwallon ƙafar duniya, za su iya tafiyar da harkokinsu a waɗannan wurare da aka keɓe ne kawai idan suna da izini daga FIFA, wato kenan manyan kamfanoni kamar su Coca Cola, Adidas ko Sony masu tallafawa FIFA ɗin ne za su ci gajiyar gasar amma ba talakawan ƙasar ba waɗanda suka yi fatan aljihunsu zai ɗan yi nauyi a lokacin gasar.

Sudan Wahlen 2010
Ƙidayar ƙuri´u bayan zaɓe a SudanHoto: AP

An gudanar da zaɓen gama gari a Sudan, amma mutane ƙalilan ne suka amince da sahihancin zaɓen, taken rahoton da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta kenan game da zabukan da aka kwashe kwanaki biyar ana yi a ƙasar Sudan. Ta ce tun a ranar farko na wannan zaɓen jam'iyun da yawa dake zama irinsa na farko cikin shekaru 24 a Sudan aka fara ganin takaici, domin sa'o'i ƙalilan da fara kaɗa ƙuri´u aka fara fuskantar ƙarancin takardun zaɓe a wasu mazaɓun. Bisa la'akari da janyewar wasu manyan jam'iyun adawa fatan samun ingantaccen zaɓe ya dakushe.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu