1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daren farko a hannun hukuma

Abdoulaye Mamane Amadou
March 4, 2021

Jagoran 'yan adawa a kasar Senegal Ousmane Sonko, ya yi daren farko a hannun jami'an tsaro, sa'o'i bayan da 'yan sanda suka tarwatsa masu boren da suka yi yunkurin kamashi a birnin Dakar.

https://p.dw.com/p/3qDMY
Senegal Präsidentschaftswahlen Wahlkampagnen Ousmane Sonko
Hoto: DW/R. Ade

An zargi Mista Sonko, da laifin tayar da hargitsi ta hayar tunzura magoya bayansa da su barke da fitina, a yayin da yake kan hanyar isa kotun birnin Dakar don saurarensa, kan wata karar da ke gabansa na tuhumar cin zarafin wata matar da ke aikin taushe a wani gidan gyaran jiki da gashi, wacce ta zargi dan siyasar da neman yi mata fyade. An shafe tsawon wunin jiya Laraba ana duki ba dadi tsakanin magoya bayan dan siyasar da jami'an tsaro, to amma duk da haka ba wani rahoton da ke tabbatar da mutuwa ko samun rauni haka da kame-kamen wadanda aka zarga da tayar da hargitsin ba.