1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier ya jaddada sukar da ya yi wa kungiyar NATO

Mohammad Nasiru AwalJune 20, 2016

Ministan harkokin wajen Jamus ya soki lamirin kungiyar kawancen tsaron ta NATO da dogaro kan karfin soji kawai maimakon neman sulhu cikin lumana.

https://p.dw.com/p/1JADd
Albanien Außenminster Steinmeier in Tirina
Hoto: picture alliance/AP Photo/H. Pustina

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya jaddada sukar da ya yi a kan manufofin kungiyar kawancen ta NATO dangane da kasar Rasha. Steinmeier ya ce yana jin tamkar kungiyar kawancen tsaron ta manta da batun musayar ra'ayoyi da tuntubar juna. Ya ce bai kamata NATO ta dogara kan karfin soji kawai ba. Da ya juya kan babban atisayen NATO shigen wanda ya gudana a kasar Poland Steinmeier ya ce bai kamata kasashen yamma sun mayar da hankali kacokan kan jibge makamai da kurarin yaki ba, abin da ke kara rura wutar rikicin da ake fama da shi. Sai dai wasu 'yan siyasar Jamus musamman na bangaren jam'iyyun CDU da CSU sun soki lamirin ministan harkokin wajen suka ce dole ya fito fili ya yi bayanin abinda yake nufi. Wasu 'yan jam'iyyun adawa sun soke shi da zama na hannun damar shugaban Rasha Vladimir Putin.