Su wane ne ke fada a rikicin Siriya?
Yakin basasan kasar Siriya ya samo asali ne daga boren juyin juya halin daya mamaye kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka a 2011. Rikicin kawo yanzu, ya janyo mayaka daga sassa saban daban na duniya.
Siriya: Dandalin tashin hankali
Tun daga shekara ta 2011 yakin basasa ya barke a Siriya bayan da bangaren kasar mafi girma ya fice daga ikon shugaba Bashar al-Assad ya koma karkashin kungiyoyi daban daban. Tuni dai yakin ya janyo hankalin kasashen ketare. Kasar ta lalace kana dumbin rayukan fararen hula da sun salwanta.
Shugaban kama karya
Rundunar sojin Siriya na goyon bayan shugaba Bashar al-Assad wadanda ke yaki domin dawo da madafan ikon gwamnatinsa a kasar baki daya. Sojojin na yaki a bangaren mayakan sakai da ke goyon bayan Assad wadanda ke samun shawarwari daga Rasha da Iran, kasashen da ke marawa Assad baya.
'Yan tawaye
Rundunar adawar ta samo asali ne daga bore da gwamnatin Assad. Akan haka ne ta hade da wasu kungiyoyi da ba na jihadi ba a fafutukar hambare gwamnatin Assad domin gudanar da zaben demokradiyya. Bayan shan wahala da yawa daga cikin mayakan sun canja sheka zuwa kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi. Duk da goyon bayan da suke samu daga Amurka da Turkiyya, karfin rundunar ta ragu matuka.
Tirjiya
Fada tsakanin Kurdawan Siriya da masu tsananin kishin addini, shi ma wani rikici ne na daban. Kurdawa da suka bazu a Turkiyya da Iran da Iraki sun jima su na fafutukar neman 'yancin kafa kasa. Kawancen sojojin da Amurka ke wa jagoranci a yaki da kungiyar IS na goyon bayan dakarun tawayen Siriya, wadanda ke hadaka da Kurdawa da mayakan sa-kan Larabawa sai dai Kurdawan basu cika yakar Assad ba.
Sabbin mayakan jihadi
Kungiyar IS ta yi amfani da rikicin yankin wajen mamaye yankunan Iraki da Siriya a 2014 inda ta ke neman kafa daularta amma dai tauraruwarta na kara dusashewa saboda munanan akidunta. IS na fuskantar kalubale a kasashen biyu bayan Amurka da Rasha sun jagoranci yaki akansu a bangare daban-daban.
Tsoffin mayakan jihadi
Ba IS ce kadai kungiyar ta'adda data addabi Siriya ba. Akwai wasu kungiyoyin tawaye masu kamar al-Qaeda da ke da alaka da Nusra Front, ko kuma Jabhat Fatah-al-Sham, wadanda ke cikin fadan Siriyar. Su na gwabzawa da juna walau da bangaren Assad ko kuma 'yan tawaye masu sassucin ra'ayi. Nusra ta hade da wasu kungiyoyi masu yawa a karkashin sunan Tahrir al-Sham tun daga watan Janairun 2017.
Tasiri daga ketare
Fadar Kremlin ta Rasha ta tabbatar da zama babbar abokiyar Assad. A watan Satumban 2015 ne sojin sama da mayakan kasa na Rasha suka hade a fadan Siriya a hukumance bayan tsawon lokaci su na taimakawa da makamai. Moscow ta sha suka daga kasashen ketare saboda yadda hare-harenta ke ritsawa da fararen hula sai shigar Rashan ta taimakawa Assad.
Kawancen kasashen yammaci
Kawancen kasashe sama 50 da suka hadar da Jamus a karkashin jagorancin Amurka ya fara kai hari kan mayakan IS da sauran 'yan ta'adda a karshen watan 2014. Kawancen dai ya raunata mayakan na IS. Amurka na da mayaka na musamman sama da dubu daya a da ke tallafawa dakarun fafutukar demokradiyya a Siriya.
Mai tsaro daga arewa
Turkiyya na bangaren kawancen da Amurka ke wa jagoranci wadda ta goyi bayan 'yan tawayen da ke adawa Assad. Ta na da danganta mai tsami da kawayenta da Amurka saboda hadin kan da Amurka ke ba wa mayakan Kurdawa wanda Ankara ke ganin na da alaka da kungiyar PKK da ke fada da Turkiyya. Sojojin Turkiyyan sun shiga fada a bangaren 'yan tawaye da ke arewacin Aleppo da Idlib.
Inuwar Farsiyawa
Iran ta goyi bayan shugaba Bashar al-Assad kafin barkewar rikici a shekara ta 2011. A kokarinta na cigaba da tasiri a yankin Gabas ta Tsakiya, Tehran ta taimakawa Damaskus da mayaka da horar da sojoji. Ita ma kungiyar shi'a ta Hezbollah da ke Lebanon na goyon bayan gwamnatin Assad kuma ta na fada a bangaren sojojin Iran da wasu mayakan gwamnati.