An saki firaiminista Abdallah Hamdok
October 27, 2021Firaiminista Abdallah Hamdok ya koma gidansa bayan ya jima a garkame a hannun sojojin da suka rusa gwamnatin riko na Sudan suka kuma yi masa daurin talala. Sakin Hamdok, na zuwa ne bayan shan matsi da kuma barazanar da Amirka da Kungiyar Tarayyar Turai suka yi, na janye duk wani tallafin da suke bai wa kasar mai fama da tarin matsaloli a sakamakon tabarbarewar tattalin arziki.
Rahotannin sun nuna yadda jama'a ke ci gaba da matsa kaimi ta hanyar zanga-zangar adawa da juyin mulkin ranar Litinin din da ta gabata. Sabon rikicin da ya kunno kai a kasar ta Sudan, ya samo asali ne daga rashin jituwa a tsakanin gwamnatin rikon kwarya da ta hada da shugabanin sojoji da na farar hula da ke iko tun bayan hambarar da gwamnatin Oumar al-Bashir shekaru biyu da suka gabata. Abdallah Hamdok ya koma gidansa tare da mai dakinsa da aka tsaresu tare inda za a ci gaba da saka ido kan kai kawonsa.