1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Al-Bashir ya saki fursunonin siyasa

Zulaiha Abubakar
April 10, 2018

Shugaban kasar sudan Omar al-Bashir ya bada umarnin sakin dukkan firsinonin siyasa da ke tsare a gidajen yarin kasar. Umarnin nasa ya biyo bayan kiraye-kirayen 'yan siyasa kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

https://p.dw.com/p/2vo4t
Omar al-Bashir
Hoto: picture alliance/AP Photo

Tun a shekara ta 2015 Bashar ke gudanar da taruka da 'yan adawa da kungiyoyin 'yan tawayen kasar don kawo karshen yakin da aka jima ana gwabzawa a yankunan kasar. A na su bangaren kungiyoyin adawa sun bayyana cewar ya zuwa yanzu akwai sauran mutane 50 da ba su samu damar shakar iskar 'yanci ba ciki kuwa harda shahararren dan siyasar nan Mohamed Mokhtar al-Khatib jagoran jam'iyyar kwaminisanci.