1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: al-Bashir ya soki masu bore

Abdul-raheem Hassan
January 27, 2019

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya caccaki masu boren neman kawo karshen shugabancinsa da cewa suna kwaikwayon salon guguwar neman sauyi da ya mamaye kasashen Larabawa a yankin Gabas ta tsakiya a shekarun baya.

https://p.dw.com/p/3CI8w
Suadan Präsident Omar Al Bashir
Hoto: Reuters/M. Abdallah

al-Bashir ya bayyana haka ne a yayin da yake ziyara a makwabciyar kasarsa wato Masar, inda ya zargi wasu kungiyoyin da ingiza wutar rikici kasashe kamar Sudan.

Hukumomi sun ce akalla mutane 30 ne suka mutu tun bayan fara zanga-zangar neman kawo karshen shugabancin sama da shekaru 30 na Shugaba al-Bashir. Amma wasu kungiyoyin kare fararen hula sun ce sama da mutane 45 ne suka mutu tun fara boren a watan Disamban 2018.

Wannan dai shi ne bore mafi muni da Shugaba al-Bashir ya fuskanta tun bayan da gwamnatinsa ta fara mulki a shekarar 1989, amma shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya sha alwashin ba da gudumuwar shawo kan matsalar da kasar Sudan ke fuskanta.