Sojoji na kashe farar hula a Sudan
January 14, 2019Talla
Kungiyar ta EU ta ce shaidu sun bayyana cewar 'yan sandar na bin jama'ar a kan tituna har ma cikin gidaje suna fatatakarsu, wasu rahotannin da aka bayyana sun ce jami'an tsaro har ckin asibiti suke kai hare-haren a zanga-zanga da kungiyoyin suka kira a karshen mako. Kungiyar kare hakin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce an kashe mutane kusan 40 a zanga-zangar ta neman shugaba Omar al-Bashir ya yi marabus, sai dai gwamnatin ta ce mutane 24 kawai suka mutu.