Takun saka tsakanin masu borai da sojoji a Sudan
June 9, 2019Talla
Likitoci na kusa da masu yi boran sun ce sama da mutane 100 suka rasa rayukansu wasu 500 suka jikata, galibi a lokacin da jami'an tsaro suke tarwatsa masu gangamin. Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da firaminista Habasha Abiy ahmed ya kammala ziyarar da ya kai a Sudan din domin shiga tsakani a rikicin tsakanin sojojin da masu yin zanga-zanga.