1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta tura jakadanta Khartoum

Ramatu Garba Baba MNA
December 4, 2019

Amirka ta sanar da bukatar bude ofishin jakadancinta a kasar Sudan a yayin da ta amince da karbar jakadan Sudan, wanda shi ne karon farko da ake samun hakan a tsakanin kasashen biyu a tsawon shekaru 23.

https://p.dw.com/p/3UElN
Sudan Neuer Premierminister Abdalla Hamdok
Hoto: Reuters/M. Nureldin Abdallah

An dai kamo hanyar gyara dangantaka tsakanin Amirka da Sudan biyo bayan hambarar da gwamnatin kama karya na Omar al-Bashir kafin a girka sabuwar gwamnatin hadaka.

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ne ya sanar da wannan ci gaban, a yayin wata ganawa da Firaiministan kasar ta Sudan Abdallah Hamdok da ya kai ziyara fadar WhiteHouse a wannan Laraba. Wannan shi ne karon farko da ake samun hakan a tsakanin kasashen biyu a tsawon shekaru 23.