1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An katse layukan waya dana sadarwa

Ramatu Garba Baba
November 17, 2021

Mutum kimanin 10 aka tabbatar sun mutu a sakamakon wani artabu a tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar adawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin rikon kwarya.

https://p.dw.com/p/436no
Sudan Port Sudan | Proteste gegen Militärregierung
Hoto: AFP/Getty Images

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa, akalla mutane goma sun mutu wasu da dama sun jikkata, sakamakon artabu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar kin jinin sojojin da suka kifar da gwamnatin riko da Abdallah Hamdok ke jagoranta. A yayin da jami'an tsaro ke musanta harbin masu boren, jami'an kiwon lafiya da ke kai dauki sun shaida bayar da kulawa ga wadanda suka ji rauni daga harbin bindiga.

Duk da an wayi garin yau Laraba da katsewar layukan waya da na hanyoyin sadarwar intanet, wannan bai hana masu adawa da juyin mulkin fitowa zanga-zangar kin jinin wannan gwamnatin da Janar Abdel Fattah al-Burhane da ya sake nada kansa a matsayin shugaban majalisar rikon kwarya ta kasar ke jagoranta ba. Sudan ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019.