An rusa jam'iyyar tsohon shugaban Sudan
November 29, 2019Ministan ministan shari'ar Sudan Nasiruddeen Albdulbari ne ya fayyace matakin dokar domin bai wa gwamnati damar dawo da haramtattun kudade da kadarorin al'umma da kusoshin jam'iyyar ta mallaka da na membobinta ta haramtattun hanya, tare da hana 'ya 'yan jam'iyyar fakewa da sunan addini don ci da gumin talakawan Sudan. Gwamntin ta haramta jam'iyyar bayan ta yi shekaru kusan 30 ana damawa da ita a madafan iko, inda daga yanzu laifi ne mutum ya ayyana kansa a matsayin memba a cikin jam'iyyar.
An gudanar da jerin gwanon nuna murna da wannan mataki, a yayin da ita kuwa jam'iyyar ta NCP cewa ta yi dokar bita da kulli ce da neman cin mutunci kawai. Sai dai wannan mataki zuwa lokacin matan kasar Sudan ke ci gaba da murnar soke wata dokar da ke hukunta mata masu yin shigar banza.
A baya an sha yi wa mata hukuncin bulala 40 da cin tara tare da dauri na watanni a gidan yari, saboda sanya wando ko tufafi masu matse jiki da shan barasa da kayyakin maye, matakin da dama daga cikin 'yan kasar ke cewa tamkar watsi da tsarin shari'a ne da tsohuwar gwamnatin Omar Hassan al-Bashir ta kaddamar a kasar.