Masu zanga-zanga sun dauki alwashin ci-gaba da zaman dirshan
May 16, 2019Talla
Hadakar jam'iyyun mai lakabin (DFCF) ta dauki alwashin ci-gaba da zaman dirshan a harabar shalkwatar tsaron kasar ta Sudan da kuma sauran gurare. Tun da fari shugaban majalisar sojojin rikon kwaryar ya sanar da cewar dakadar da tattaunawa da masu zanga-zangar ta zamo wajibi biyo bayan karya ka'idar da bangarorin biyu suka shardantawa kansu gabanin cimma matsaya da masu zanga-zangar su ka yi.