Ana ci gaba da fafautukar samar da gwamnati
May 18, 2019Talla
Lamarin da ke zuwa bayan sanarwar dage zaman da aka yi a sanadiyar sabanin ra'ayi. A ranar Laraba da ta gabata, majalisar mulkin soja ta wucin gadi da wakilan masu zanga-zanga, sun amince da wata yarjejeniya da ke da nufin kafa gwamnatin riko ta tsawon shekaru uku, wadda za ta kai kasar ga tsarin mulkin dimukuradiyya.
A wannan Asabar ma, akwai dubban masu zanga-zanga a harabar hedkwatar soji da ke birnin Khartoum, da ke son ganin, lallai sai sojojin sun mika mulki hannun farar hula. Watanni biyar aka kwashe ana zanga-zangar adawa da mulkin al-Bashir, da ta kai ga samun asarar daruruwan rayukan, kafin a kai ga kifar da gwamnatinsa na fiye da shekaru talatin.