Shugaban Sudan ya karyata zargin da ake masa
January 20, 2019Talla
Dama dai kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi jami'an tsaron kasar da amfani da karfi kan masu zanga-zangar duk kuwa da cewar Shugaba Omar al-Bashir ya dora alhakin wadanda suka rasa rayukansu kan bata garin da ya ce sun fake da zanga-zanar don jefa kasar cikin rudani yayin da ya halarci wani gangami a birnin Al-Kurreda. Sabuwar zanga-zangar ta balle yayin da ma'aikatu dabam-dabam da kuma kungiyoyin Likitoci da Lauyoyi da masu hada magunguna suka tsunduma yajin aiki.
A daya bangaren Shugaba al-Bashir wanda ya dare kan madafun iko ta hanyar juyin mulki shekaru 30 da suka gabata na ci gaba da jaddada akwatin zabe a matsayin hanyar canza gwamnati a kasar.