Sudan: Burhan ya sake nada kansa shugaban rikon kwarya
November 11, 2021Babban hafsan sojin Sudan Janar Abdel-Fattah Burhan ya sake nada kansa mukamin shugaban rundunar soji a majalisar rikon kwarya da sojojin ke jagoranta, abin da ke nuna alamar yana kara karfafa ikonsa a kasar makonni biyu bayan da ya jagoranci juyin mulki da ya hambarar da shugabannin farar hula.
Ya yi biris da matsin lambar da ake yi masa a cikin gida da kuma kasashen duniya na mayar da kasar kan tafarkin dimukuradiyya.
Sabuwar majalisar rikon kwaryar mai wakilai 14 ta kunshi wakilan farar hula sai dai babu wakili ko daya daga kungiyar neman sauyi ta Forces of Freedom and change FFC wadda ke cikin hadakar gwamnatin rikon kwarya da suka raba mukamai da sojoji tun 2019.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga kungiyoyi masu rajin cigaban dimukuradiyya kan matakin na Janar Abdel Fattah Burhan.
Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da sojojin suka yi alkawarin mayar da mulki ga hannun farar hula.
Tun bayan juyin mulkin na ranar 25 ga watan Oktoba an tsare jami'an gwamnati da shugabannin siyasa fiye da dari daya tare da yan zanga zanga da masu fafutuka da dama.