Sudan da Sudan ta Kudu sun koma Tattaunawa
September 4, 2012Yayin da rage makonnin ukku wa'adin da ƙungiyar Tarrayar Afirka ta shata wa ƙsasahen, na su sasanta ko kuma ta hukumta su ,ya ke cikka a ranar 22 ga wannan wata.Ƙungiyar dai ta Tarrayar Afirka ta ƙara tsawaita wa'adin wanda a da, ta tsaida shi a ranar biyu ga watan Agusta da ya wuce.Rahmtullah Osman shi ne ministan harkokin waje na Sudan ya kuma bayyana abin da taron zai tattauna.
Ya ce ''batun raba kan iyaka tsakanin Sudan da Sudan ta kudu da maganar tsaro, da rikicin yankin kudancin Kordafan ;da gokin Nilo, da kuma rabon arzikin albarkatun man fetur tsakanin ƙasahen biyu shi ne ke cikin ajendar taron''.A farkon watan jiya hukumomin Sudan da juba suka rataɓa hannu akan wata yarjejeniya na biyan kuɗaɗen diya na fiton mai da Sudan ta kudu zata riƙa biya ga ta Arewa.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu