Sudan: EU ta tsame hannunta daga zaben kasa
April 9, 2015
Kantomar harkokin waje ta EU din Federica Mogherini ta ce rashin cimma daidaito tsakanin al'ummar kasar da shugaba el-Bashir ya yi da gallazawa 'yan adawa da masu fafutakar kare hakkin dan Adam su ne za su kasance ummul aba'isin gaza samun sakamako na gari a zaben na Sudan.
Wannan hangen da EU din ta ce ta yi ne ma ya sanya Ms Mogerini ta ce EU din ba za ta bada wani tallafi ko tsoma baki a zaben Sudan din ba sai dai ta ce za su cigaba da dafawa kungiyar kasashen Afirka ta AU a yunkurinta na ganin an samu zaman lafiya a kasar.
Shugaba el-Bashir dai zai yi takara ne da mutane 15 galibinsu daga kananan jam'iyyu yayin da manyan jami'yyun adawa na kasar suka ce ba za su shiga zaben ba, dalilin da ya sanya ake ganin ba makawa shugaban zai samu nasara a zaben.