Sudan: Fada ya barke da sojoji a Khartoum
April 15, 2023Talla
Rundunar tsaron ta RSF ta yi ikrarin karbe iko da fadar shugaban kasa da kuma filin jirgin sama a wani abu mai kama da yunkurin juyin mulki.
Sai dai sojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al Burhan a cikin wata sanarwa ta ce ta karbe ragamar shugabancin kungiyar ta RSF ba tare da wata turjiya ba.
Sojojin sama na Sudan sun kai farmaki sansanonin RSF inda suka fattake su a cewar sanarwar rundunar sojin.
Rundunar sojin Sudan din dai ta baiyana dakarun na RSF a matsayin runduna ta yan tawaye.