1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun halaka a gobara a Sudan

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 3, 2019

Kimanin mutane sama da 20 ne suka halaka sakamakon tashin gobara a wata masana'antar sarrafa tile da ake yin daben gida na zamani da shi, a Khartoum babban birnin kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/3UAZo
Gobara ta halaka mutane a wata masana'anta a Khartum
Gobara ta halaka mutane a wata masana'anta a KhartumHoto: Reuters

Majalisar zartaswar kasar ta Sudan ta nunar da cewa gobarar ta kuma raunata wasu mutane 130, inda wasu ke cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai, abin da ya sanya fargabar yiwuwar karuwar adadin wadanda suka mutu. Tuni dai aka garzaya da wadanda suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi sanadiyyar fashewar da wata tankar dakon iskar gas ta yi, a yayin da take sauke gas din a masana'antar zuwa asibiti.