Sojojin Sudan za su mika mulki bayan cimma matsaya
November 21, 2021Talla
A wata sanarwar da ta fito yanzu ta hannun Fadlallah Burma Nasir, wanda shi ne shugaban jam'iyyar Umma, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, Hamdok zai dawo mukaminsa zai kuma kafa majalisar ministoci mai zaman kanta nan bada jimawa ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, a wannan Lahadin, za a saki duk wadanda ake tsare da su kamar yadda aka cimma a karkashin yarjejeniyar da aka kulla a yammancin jiya Asabar. Masu zanga-zangar sun tsaya kai da fata na ganin an maido da gwamnatin riko ta farar hula da Hamdok ke jagoranta bayan da Janar Abdel Fattah al-Burhane ya jagoranci juyin mulki tare da nada kansa a matsayin shugaban majalisar rikon kwarya ta kasar ya hambarar.