1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matar da ta kashe mijinta ta sami sassaucin kotu

June 26, 2018

Kotu a Sudan ta sassauta hukuncin farko da ta zartas kan matashiyar nan da aka samu da laifin kashe mijinta a yayin da yake ma ta fyade, Nour Hussein za ta yi zaman gidan yari na shekaru 5 tare da biyan diyya.

https://p.dw.com/p/30LTB
Indien - Kinderheirat
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Hatvalne

An sami matar da yanzu ke da shekaru goma sha tara da laifin kisan ne bayan da ta dabawa mijin na ta wuka a lokacin da ya ke tsakiyar yi ma ta fyade tare da taimakon wasu 'yanuwansa da suka rike ta, bayan ta ki amincewa ya tara da ita a auren dole da aka yi mata.

Hukuncin kotun na farko ya ja hankulan duniya inda kungiyoyi masu adawa da hukuncin kisa dama wasu da masu zaman kansu da suka yi ta fafutuka don ganin kotu ta yi adalci na yin watsi da hukuncin na kisa.