1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Jami'an tsaro sun tarwatsa masu bore

Ahmed Salisu
August 17, 2020

Jami'an tsaron Sudan sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tarwatsa masu zanga-zanga da suka hadu dazu a birnin Khartoum don tunawa da ranar da aka cimma yarjejeniya ta girka gwamnatin hadin kan kasa.

https://p.dw.com/p/3h6Xj
Unruhen im Sudan | Demonstration
Hoto: picture-alliance/Photoshot

Masu zanga-zangar dai sun yi ta kone-kone na tayoyi tare da yin kiraye-kiraye ga masu rike da madafun iko kan su matsa kaimi wajen yin gyare-gyare na yadda ake tafiyar da kasar kamar yadda aka amince a shekarar da ta gabata.

Wasu daga cikin abubuwan da aka amince da su a bara sun hada da shirya zaben da zai bada dama ta girka gwamnatin farar hula cikin watanni 39 da kuma girka majalisar dokoki gami da nada fararen hula a matsayin shugabannin wasu kamfanin kasar sojoji ke jagoranta.

Gaza kaiwa ga aiwatar da wadannan gyare-gyare da aka amince da su inji masu zanga-zangar zai sa su kasance ba su da wani zabi illa cigaba da fantsama kan tituna a kulli yaumin don yin bore.