1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Janar Ibn Auf ya yi murabus

Gazali Abdou Tasawa
April 14, 2019

Shugaban hukumar mulkin soja ta rikon kwarya a Sudan Ahmed Awad Ibn Auf ya yi murabus daga kan mukaminsa a bisa matsin lambar masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/3GiLT
Sudan | Awad Ibn Auf als Präsident des militärischen Übergangsrates vereidigt
Hoto: picture-alliance/AA

Ibn Auf ya bayyana yin murabus din nasa ne a wani jawabi da ya gabatar wa 'yan kasar a jiya Juma'a inda kuma kai tsaye ya sanar da maye gurbinsa da Abdel Fattah al-Burham Abdelrahmane babban speto na rundunar sojin kasar, kana ya sanar sauke Janar Kamal Abdul-Murof al-Mahi mataimakin shugaban kasa daga mukaminsa. Jama'a dai sun fantsama a saman titunan birnin Khartoum suna bayyana farin cikinsu da wannan nasara da suka yi ta kifar da shugabannin biyu a cikin kwanaki biyu kacal. 

A ranar Alhamis da ta gabata ce sojojin kasar ta Sudan a karkashin jagorancin Awad bin Auf ministan tsaro kana mataimakin Tsohon Shugaban kasa Omar Al-Bashir wanda ya share shekaru 30 kan karagar mulkin kasar, suka karbe mulki tare da kafa wata hukumar sojoji wacce za ta yi mulkin rikon kwarya na shekaru biyu. Sai dai al'ummar kasar ta Sudan ta ci gaba da boren nuna rashin amincewa da shugaban rikon wanda ta ce shi kansa yana da balshe, sannan tamkar kwaryar sama da ta kasa shi da tsohon shugaba da ya sauke daga kan mulki.