1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar kafa gwamnati a Sudan

Ramatu Garba Baba
May 15, 2019

Bangarori masu jayayya kan shugabanci a Sudan sun sanar da cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin riko ta farar hula ta shekaru uku, bayan da aka kwashe makwanni ana kai ruwa rana kan irin gwamnatin hadakar da za a kafa. 

https://p.dw.com/p/3IVq8
Afrika | Protests im Sudan
Hoto: picture-alliance/dpa/AA/M. Hjaj

An dai samu nasara cimma matakin dinke barakar da aka samu tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Oumar Hassane al-Bashir. Bangarorin biyu na sojoji da masau zanga-zanga, sun amince da a kafa gwamnatin rikon kafin shirya zabe, inda tuni suka fitar da wata sanarwar hadin gwiwa ga manema labarai. Masu zanga-zangar dai sun taka gagarumar rawar da ta kawo karshen mulkin shekaru 30 na tsohon shugaban kasar. Matakin sojojin da suka hambarar da shi na ci gaba da rike mulki na tsawon shekaru biyu kafin a gudanar da zabe, ya fusata masu boren da suka dage kan a mika mulkin hannun farar hula.