Nemat ta zama babbar alkalin Sudan
October 11, 2019Talla
Nemat Abdullah Khair shararriyar lauya ce da ta shafe kusan shekaru 40 tana aikin alkalanci a Sudan, kuma ta kasance mace ta farko da ta fara rike mukamin babban alkali a kasar.
Kakakin gwamnatin hadakar soji da ta farar hula a Sudan Mohammed al-Fakki Solimon ya ce an tabbatar da Taj al-Ser Ali al-Hebr a matsayin babban mai shigar da kara. A watan Afirilun shekarar 2019 ne aka kawo karshen gwamnatin Omar al-Bashi na tsawon shekaru sama da 30, bayan jerin zanga-zangar neman sauyin gwamnati.