Zanga-zangar Sudan ta dauki sabon salo
April 6, 2019Talla
Tun da safiyar wannan Asabar, dubban masu zanga-zanga suka soma yin maci a babban birnin kasar Kahrtoum, inda da yawa daga cikinsu suka kai hedlkwatar rundunar sojan kasar, wanda shi ne tattaki irinsa na farko tun bayan fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin shugaban al-Bashir a shekar bara.
Masu zanga-zangar da suka yi dafifi a sansanin sojin kasar da ke birnin Khartoum da fadar shugaban kasar sun mayar da martani da jifan 'yan sandan da suka nemi hana su shiga. An dai zabi wannan rana ta yau wato 6 ga watan Afrilu ta zama ranar maci na kasa baki daya don a ranar ce a shekarar 1985 wani juyin mulki ya kifar da gwamnatin Shugaba Jaafar Nimeiri.